Labarai

An Kaiwa Tawagar PDP Hari Akan Hanyarsu Ta Zuwa Taron Jam’iyya Na Kasa

PDP ta ce tana so ayi bincike a kan al’amarin

Mutanen da aka kai ma hari na cikin tawagarta daga jihar Lagas

Hotuna sun nuna wata motar bas dauke da hujin harbin bindiga

Jam’iyyar PDP ta koka kan wani hari da aka kai ma wasu mambobinta a hanyarsu ta zuwa Abuja don taron jam’iyyar na kasa a karshen wannan mako. 

 

Jam’iyyar ta adawa ta bayyana cewa ta shiga alhini bisa wannan al’amari sannan kuma ta yi kira ga ayi bincike cikin al’amarin.

“Mun shiga alhini kan harin da wasu yan bindiga suka kai ma wasu tawagar PDP daga jihar Lagas, wadanda ke a hanyarsu ta zuwa Abuja don halartan taron jam’iyyar.

“Wannan abun bakin ciki ne da ba’asa masa rana. Muna kira ga hukumomin tsaro da suyi bincike cikin al’amarin sannan kuma a gurfanar da masu laifi.

“Muna taya wadanda abun ya safa bakin ciki bisa wannan harin tozarci sannan kuma muna kira ga mambobin jam’iyyarmu a jihar Lagas da sauran jihohin da su kasance masu jajircewa.”

 

Souce In Naij

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.