Labarai

An kai karar Kim Kardashian saboda satar jakar selfie

Kardashian is regularly seen promoting and using the LuMee case

An kai karar kamfanin Kim Kardashian West saboda satar fasahar jakar selfie.

Jakar saka wayar komai-da-ruwanka ta LuMee, wacce kamfanin Kimisaprincess Inc ke tallatawa, tana da wata fitila da ke taimakawa masu amfani da ita wurin daukar hoton dauki-da-kanka, selfie, mai kyau.

 

Amma wani mutum mai suna Hooshmand Harooni ya bukaci ta biya shi $100m (£75m) saboda satar fasaharsa.

Ya ce shi ne ya “kirkiro fitila da kuma jakar ta wayar salula” a shekarar 2013, wadda aka yi wa lasisi a kamfanin Snaplight.

Mr Harooni ya ce satar fasahar da LuMee ya yi masa da kuma tallata shi da Kardashian ke yi sun sa ya yi asarar makudan kudi.

Kardashian na karbar wani bangare na ribar da LuMee ke samu, a cewar wasu takardun kotu.

Wata sanarwa da mai kamfanin Snaplight, Bardia Rahim ya fitar ta ce LuMee ya “sanya mana shakku a fasaha da kuma yadda muke tafiyar da lamuranmu” saboda kaddamar da jakar da ya yi.

“Bai kamata ya yi wa harkokin kasuwanci irin wannan ba, bayan haka kuma wannan dabi’ar ta yaudara ba dabi’ar Amurka ba ce,” in ji shi.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.