Labarai

KADUNA: Akwai Lauje Cikin Nadi A Kwamitin Tantance ‘Yan Takara Na APC

Kwamitin tantance ‘yan takara na jam’iyyar APC mai kula da zaɓukan fidda gwani na kananan hukumomin Jihar Kaduna ya fitar da sunayen ‘yan takara waɗanda suka yi nasara da wadanda basu samu nasara ba a zaɓen da zai gudana a ranar 5 ga watan Mayun shekara ta 2021.

Ɗaya daga cikin ‘yan takarar shugabancin ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu Honorabul MS Ustaz Mesittin na ɗaya daga cikin waɗanda suka samu zana jarrabawar gwaji da jam’iyyar ta shirya kuma ya yi nasarar samun maki 53.38. Wanda hakan ke nuna cewar ɗan takarar ya tsallake, amma abin mamaki sai gashi bayan fitar da sunayen an cire sunan MS Ustaz cikin wadanda suka yi nasara.

Wani abin mamaki shine sai gashi wasu ‘yan takara guda biyu Rabi’u Aliyu da Sabo Aminu Anchau daga ƙaramar Hukumar Kubau an bayyana su matsayin waɗanda suka yi nasara da maki 50 da 53 kowanne ɗaya daga ciki. Wannan wani al’amari ne mai muhimmanci da ya kamata jam’iyya ta yi la’akari dashi.

Yana da matuƙar muhimmanci babbar jam’iyya kamar APC tayi dukkanin mai yiwuwa wajen samun haɗin kan ‘ya’yan jam’iyya ba raba kawunan su ba, domin tabbas wannan rashin adalci da aka yi zai haifar da gagarumar matsala a jam’iyyar.

Abin da ake fata shine jam’iyyar ta kare muradun ‘ya’yanta ta hanyar adalci ba biye wa son zuciyar wasu shafaffu da mai a cikin jam’iyyar ba, duk wanda ya yi nasarar a jarrabawar da aka yi a bashi damar yin takara.

Bisa ga wannan ne muke kira ga mai girma Gwamnan Jihar Kaduna, da Jam’iyyar APC ta Jihar da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, da su shigo cikin lamarin su tabbatar anyi adalci ta hanyar ba da dama ga dukkanin waɗanda suka cancanci yin takara a basu damar tsayawa takara domin kai wa ga nasarar jam’iyyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: