Kadan Daga Cikin Amfanin Tashar Jiragen Ruwa Na Minna

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kadan daga cikin amfanin tashar jiragen ruwa na Baro sea port da Shugaba Buhari ya bude (Asabar 19-01-2019).
******************************
Wannan tashar jiragen ruwa da Shugaba Buhari yayi kuma ya bude, shine na farko a Arewacin Nigeria, shugaba Buhari ya fara aikin tashar ruwan Baro a lokacin da yake mulkin soja a 1984, sai dai gwamnatin General Ibrahim Badamasi Babagida data kifar data Buhari bata cigaba da aikin ba a tsawon shekaru 8 da Babangidan yayi, duk kuwa da cewa a jihar sa ne aikin, babu wata gwamnati data sake duba aikin Baro port sai da shugaba Buhari ya dawo mulki a 2015 bayan shekaru 32 da fara aikin, sai dai a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa marigayi Alhaji Ummaru Musa ‘Yar Adua (Allah yaji qan sa da rahama) ya bayar da aikin zuwa jihar Kaduna.
.
‘Yar Adua ya fara yashe Kogin river Niger domin yazo har Kaduna, don samar da tashar jirgin ruwa, a lokacin ya bayar da tsaban kudi kawai na aikin har Naira biliyan 19, amma bayan Allah ya karbi ran sa, Goodluck Jonathan yana hawa mulki, saboda mugunta da tsanar Arewa da ‘yan Arewan, sai ya bayar da umarnin a a dakatar da aikin kuma a debe kudaden a zuba su a ma’aikatar raya yankin Niger – Delta, haka kuma akayi, da taimakon PDP da ‘yan Arewan da suke cikin ta aka daga aikin daga Arewa, tun daga nan ‘yan Arewa suka cire tsammanin samun tashar jirgin ruwa a yankin mu na Arewa.
.
Da yake Allah baya zalunci sai Allah ya tausaya wa wannan yanki na Arewa ya kawo mana Shugaba Muhammadu Buhari (mai alheri) ya tone kogin River Niger har zuwa Baro dake cikin jihar Niger ya hada shi dana River Niger, Alhamdulillah wannan rana rana ce ta tarihi a Arewa (19-01-2019 Asabar) Shugaba Buhari ya bude tashar wacce aka yi ta akan kudi Naira Biliyan 6, daga cikin amfanin wannan tashar.

1. Gwamnati zata dauki ma’aikata har dubu biyu.

Talla

2. Sannan mutane kusan miliyan uku zasu samu aiyukan yi ta sanadin wannan tashar.

3. Manyan jiragen ruwa daga Kasashen Turai dana Larabawa da kuma Yankin Asia zasu iya shigowa har Arewacin Nigeria su sauke kaya ko su dauki kaya.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

4. Sannan ‘yan kasuwan Arewa da suke zuwa China su sayo kaya a jirgin ruwa a sauke musu a Lagos daga nan su dauko zuwa Arewa Yanzu zasu huta da zuwa Lagos.

5. Farashin kayan kasashen waje a Arewacin Nigeria zai ragu matuka sosai, saboda dama dauko kaya daga tashar jirgin ruwan Lagos zuwa Arewa yana tilasta yan kasuwa dole su kara kudin kaya, yanzu zuwa Lagos ya kare in sha Allah indai don dauko kaya ne.

Allah kayi albarka wa Shugaba Muhammadu Buhari, ka kara masa nasara, ka kara bashi makusanta nagari.
By…..
Abdulhadi Isah Ibrahim.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: