Labarai

Kabiru Gombe Zai Maka Tsohon Kwamishinan Kano A Kotu

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya lashi takobin daukar matakin shari’a kan tsohon Kwamishinan Ayyukan Jihar Kano, Muaz Magaji, kan neman bata masa suna.

Sheikh Kabiru Gombe ya yi barazanar ce bayan tsohon kwamishinan ya wallafa a Facebook cewa yana da sautin wata tattaunawa a tsakanin Kabiru Gombe da Shugaban Rikon Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni.

Ya yi ikirarin cewa a cikin sautin da aka tatsa ta wayar tarho, an jiyo Kabiru Gombe na barazanar barin APC matukar shugabanninta suka bari Kwankwaso ya dawo jam’iyyar.
Amma, Sheikh Gombe ya musanta zargin da cewa ba komai ba ne face labarin kanzon kurege, ya kuma ba wa tsohon kwamishinan awa12 ya fito fili ya janye kalamansa tare da neman afuwar malamin ko kuma ya maka shi a kotu a kan neman bata masa suna.

Har wa yau, shehin malamin ya ce babu wata alaka tsakaninsa da duk wani ofishi, alaka daya gare shi, ta kasancewarsa Musulmi.

Magaji dai ya yi kaurin suna wurin tayar da kura ta hanyar sakonnin da yake wallafawa, musamman a Facebook.

Idan ba a manta ba, Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya taba sallamar shi daga mukaminsa a watan Afrilun 2020, bayan wasu kalamai da ya yi da ke nuni da jin dadin rasuwar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari.

Sai dai Magajin ya musanta zargin da aka masa, daga baya aka sake nada shi wani mukamin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: