Labarai

Ka Taimaka Ka Yi Min Adalci, Rokon Abduljabbar Kabara Ga Gwamna Ganduje

Daga Indabawa Aliyu Imam

Shahararren mai hawa mumbari a jihar Kano Abduljabbar Nasiru Kabara ya roki gwamna Ganduje da ya yi masa adalci cikin matakin da ya zartar a kansa.

Abduljabbar Kabara wanda gwamnatin Kano ta bayar da umarnin rufe masallacin da yake karatu tare da dakatar da shi daga dukkan wani karatu ko motsi a jihar ta Kano ya yi wannan kira ne ga gwamnatin Kano domin ta sassauta masa matakin da ta zartar wanda ya bayyana shi a matsayin rashin adalci a wata tattauwa da yayi jiya da gidan jaridar BBC.

” Ina kira ga hukuma musamman shi mai girma gwamnan Kano Khadimul Islam yadda yake kwatanta adalci, ina rokon sa ya kara tsayawa a kan adalcin nan ya hada mu zama da malamai domin mu tattauna.” Cewar Abduljabbar Kabara.

Tun da jimawa ne malamai daga bangarorin addinin musulunci a Kano da sassan kasar nan ke zargin Abduljabbar da batancin ga janibin Annabi S.A.W tare da aibata sahabbansa da matansa, wanda hakan ya sa da dama daga cikinsu aika masa da sakon muqabala wacce suka ce yaki amsa gayyatar tasu sai dai Abduljabbar yayi martani ga kalaman nasu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: