Ka Fito Ka Bayyana Sunayen Sarakunan Dake Da Alaka Da Barayin Shanu Ko Mu Ladabtar Da Kai -Inji Sarakunan Zamfara


0 246

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Majalisar sarakunan jihar zamfara, karkashin jagorancin Alhaji Attahiru Ahmad, sun ja kunnen ministan tsaro Mansur ‘Dan Ali, kan abinda suka kira zargi da kazafi, da yayi masu na cewa sarakunan suna da hannu dumu-dumu kan harkar barayi.

Majalisar sun Bukaci Mansur ‘Dan Ali da ya fito ya bayyanawa duniya sunayen sarakunan da ake zargin su da yin tarayya da barayi a jihar, Kazalika sun bayyana cewa matukar munistan tsaron bai fito ya tona asirin wadannan sarakunan ba Shakka Babu za su dauki matakin ladabtarwa, a matsayin sa na ‘Dan su.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Sun cigaba da cewa jami’an tsaro Sun kasa isa inda barayin suke, kuma Boma-baman da sojoji suka jefa a wasu kauyuka kamar karamar Hukumar Gusau, da Kauyen Tangaran, da ke karamar hukumar Anka, da kuma Dumburun, a karamar hukumar Zurmi, duk ba nan ne Maboyar Barayin ba.

Sannan Sun Kara da cewa mafiya yawan wadanda aka kashe mutanene da ba su ji ba basu ganiba, ne jami’an tsaron Sun kashe jama’a da dama, kuma wasu da dama sun jikkata, ba Bisa Hakki ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.