Gwamnan jihar Bauchi, Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ya bukaci dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da jam’iyyarsa, kan su rungumi kaddara bisa kaye da suka sha a zaben shugaban kasa na 2019 tare da kira gare su da su mara wa gwamnatin Buhari baya domin ci gaban kasar nan.
Gwamnan ya yi wannan kira ne a cikin sanarwar ga manema labarai da sakataren yada labarai na gwamnan, Abubakar Al-Sadikue, ya sanya wa hannu.
Gwanman ya kara da cewa, “demokradiyya tana tafiya ne ta bai wa masu zabe damar zaban wanda suke so ta hanyar jefa kuri’a.”
Gwamnan ya yi nuni da cewa zaben Buhari nufi na Allah inda ya yi kira ga ‘yan adawa da su rungumi kayen da suka sha da zunciya daya.
Ya tunatar da ‘yan Nijeriya cewa shugaba Buhari na da kyawawar manufq na inganta rayuwarsu.
Barista Muhammad ya ba da tabbacin goyon bayansa da na ‘yan jihar Bauchi ga duk wani kudirin shugaban kasa.
Ya bukaci jama’ar jihar da su fito kwansu da kwarkwatansu don’t kada kuri’a a ranar 9 ga wannan wata.