Ana saran jirgin saman da zai mayar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari gida zai sauka a filin jirgin saman Abuja da misalin karfe 4:30 na yamma a agogon kasar, kamar yadda wani jami’in fadar shugaban kasar ya shaida wa BBC.
A safiyar Asabar ne fadar Shugaban Najeriya ta ce shugaban zai koma gida bayan wata doguwar jinya a birnin Landan.
”Ya gode wa daukacin ‘yan Najeriya wadanda suka yi ta yi masa addu’ar samun lafiya da fatan alheri tun lokacin da ya fara jinya,” in ji wata sanarwar da Mai bai wa shugaban Shawara kan watsa labarai Femi Adesina ya aiko wa BBC.
Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017
- 19 ga watan Jan – Ya tafi Birtaniya domin “hutun jinya”
- 5 ga watan Fabrairu – ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
- 10 ga watan Maris – Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
- 26 ga watan Afrilu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma “yana aiki daga gida”
- 28 ga watan Afrilu – Bai halarci Sallar Juma’a ba
- 3 ga watan Mayu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
- 5 ga watan Mayu – Ya halarci sallar Juma’a a karon farko cikin mako biyu
- 7 ga watan Mayu – Ya koma Birtaniya domin jinya
- 25 ga watan Yuni – Ya aikowa ‘yan Najeriya sakon murya
- 11 ga watan Yuli – Osinbajo ya gana da shi a London
- 23 ga watan Yuli – Ya gana da wasu gwamnonin APC da shugaban jam’iyyar
- 26 ga watan Yuli – Ya sake ganawa da wasu gwamnoni ciki har da na PDP
- 4 ga watan Agusta- Ya gana da Archbishop na Canterbury, Justin Welby
- 13 ga watan Agusta – Ya gana da wasu daga cikin jami’an gwamnatinsa
- 18 ga watan Agusta – Ya gana da Fasto Enoch Adeboye.
- Allah yasa Alkairee ne dawo warsa
Add Comment