Jiragen Yaki Najeriya Sunyi Ruwan Wuta Akan Tawagar Boko Haram

1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Assalafy

Maimagana da yawun rundinar sojin saman Nigeria Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayyana sanarwan cewa wasu jiragen leken asiri sun leko tawagar ‘yan Boko Haram/ISWAP sun taru suna tattaunawa a wani yanki da ake kira Kolloram dake yankin Tafkin Chadi a jihar Borno

Talla

Bayan jiragen leken asirin sun gano ‘yan ta’addan shine sai aka tura manyan jiragen yaki Alpha Jet dauke da manyan bama-bamai da roket sukayi ruwan wuta akan tawagar ‘yan Boko Haram din

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

‘Yan ta’addan sunyi amfani da bindigar da ake harbo jirgin sama wato Anti-Aircraft (AA) don su harbo jirgin amma ba su kai ga nasara ba, jiragen yakin sun jefa musu manyan bama-bamai kuma an hallaka adadi mai yawa daga cikin ‘yan ta’addan tare da rushe gine-ginen da sukayi a yankin

Muna rokon Allah Ya karawa rundinar sojin Nigeria nasara akan ‘yan Boko Haram Amin

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: