Jiragen Yaki Da Nijeriya Ta Sayo Daga Amurka Sun Iso Gida
Jiragen yakin da Shugaba Buhari ya nemi Amurka ta sayar wa Nijeriya a 2016 sun iso Nijeriya yau Alhamis da safe.
Jiragen wadanda aka kera su na musamman domin kai hare hare cikin dare tare da dauko hoton abubuwan da suke nesa (kilometres 35), Nijeriya ita ce kasa ta uku da Amurka ta yarda ta sayar mata da wadannan jiragen bayan Brazil da Saudi Arebia.
Shugaba Buhari ya mika kudaden su tun a 2016, an samo tsaiko ne saboda kin amincewa da wasu tsare tsare da Nijeriya ta yi, akwai ka’idar da Amurka take so a yi amfani da jiragen, wanda Nijeriya ba ta yarda da su ba, sai bayan da aka yi zama mai tsawo kafin aka kai ga sayar da jiragen wa Nijeriya ba tare da cika wancan sharadi dari bisa dari ba.
An bayyana cewa jiragen za su taimaka sosai wurin gano masu garkuwa da mutane tare da maboyarsu.
Daga AMINU MUSA ADO KARAYE
Add Comment