Labarai

Jinjina Ga Matasan Da Suka Fatattaki Charly Boy A Abuja

Daga AbdulRa’uf Matawalle (Sarkin Yakin Baba Buhari)

Jinjina da mika sakon godiya ga matasan da suka suburbudi dan iskan garin Abuja Charly Boy.

Wannan shike nuna mana har gobe da jibi matasa sun san gaskiya kuma suna tare da Baba Buhari dari bisa dari.

Kuma izina ne ga jami’an tsaro.

Don duk abin da ke faruwa a Nijeriya sakacin sune.

Don a Nijeriya ne kotu ta saki Babban dan ta’adda mai fafutukar kafa kasa a cikin kasar Nijeriya.

 

A Nijeriya ne dan ta’adda ya sanar da sojojin sa da ‘yan sandan sa da ministocinsa.

Amma saboda kabilanci da renin hankali kotun da ta bada belin sa har yanzu ba ta bada dokar kamo shi ba.

Baya ga karya dokokin da ta gindiya masa. Saboda tsoron Isra’ila.

Kuma ga duk mai hankali da tunani ya san Nnamdi Kanu ya fi Shekau aibu.

Saboda dalilai masu dama, ko kuma na ce layin su da Shekau kusan tafiyar daya ce.

Amma abin takaici Gwamnati ta ki cewa komai.

Allah wadan naka ya lalace.

Allah don kudura da arada ka gaggauta baiwa Baba Buhari lafiya mai dorewa.

Allah duk masu hannu a Boko Haram da Biafara da Niger Delta Allah ka saukarwa dukiyar su masifa da lafiyarsu.

Kuma ina kara baiwa gwamnati shawara da ta gaggauta sakin shugaban ‘yan shi’a Sheik Ibrahim Zakzaky da Dasuki, tunda ba shari’a ake yi na adalci ba, shari’ar tsoron Isra’ila ne.