Get New DJ Mixes
Kiwon lafiya

Jijjiga Jarirai Na da Mummunan Hatsari

Sama da jarirai 220 ne suka muka mutu a Burtaniya dalilin jijjiga su da aka yi a shekara 10 da suka wuce, a cewar wani bincike da kungiyar NSPCC ta yi.
An yi bitar lamarin da ya faru da jarirai 1,253, inda kusan daya cikin shida na jariran ya nuna cewar ya samu rauni ne a kwakwalwarsa.
Kungiyar ta ce a ganinta, wadannan alkaluma “somin tabi” ne.
An gudanar da binciken ne a matsayin wani kamfe a yankin Yorkshire don wayar da kan iyaye su daina jijjiga jariransu.
Dakta Suzanne Smith, wata tsohuwar malamar jinya a Leeds ta kafa shirin kuma ta ce: “Na ga mummunan tasirin da jijjiga jarirai ke yi a asibitoci- inda jarirai suka sha mutuwa ko kuma su kamu da munanan ciwuka da kan haifar da nakasa don haka dole ne mu tashi tsaye mu hana hakan aukuwa.”
Dan Joanne Peacock, mai suna Charlie ya zama galhanga kuma ya makance bayan da mahaifinsa ya jijjiga shi a gidansu da ke Huddersfield lokacin yana dan wata hudu.
“Na fito daga wanka na samu Charlie ya sauya launi, kamar ba shi da rai, ba ya numfashi a hannun mahaifinsa wanda kuma bai yi min wani bayani ba.
“Ba mu yi tunanin za mu kai asibiti da ransa ba.
“Sun gaya mana cewa mu yi shirin samun labari mai muni, sannan kuma raunin da ya samu daidai yake da a ce ya same shi a hatsarin mota saboda an jijjiga shi da karfin gaske.”
An tsare tsohon mijin nata tsawon shekara 4 a 2009 bayan da amsa laifin yi wa jaririn rauni.
Ta ce yanzu Charlie, mai shekara 12 ya girma kuma ya zama yaro mai kawo wa iyalinsu farin ciki amma ba komai yake iya yi ba kuma har karshen rayuwarsa, za a rika ba shi kula ta musamman.
Yanzu, Joanne Peacock ta zama mai wayar da kan mutane kan illolin jijjiga jarirai.
“Abu mafi muhimmanci a gare ni dangane da abin da ya samu Charlie shi ne rage yawan jariran da irin haka ke faruw ada su,” a cewarta.
John McMullan, wani kwararren likitan kwakwalwar yara a asibitin yara na Sheffield ya ce jijjiga jariri na janyo raunuka a kwakwalwa iri daya da wanda akan samu a wasan dambe.

Elaine Hanzak ta tuna yadda a ranar ta dimauce, cikin kankanin lokaci ta sauya daga kasancewa cikin farin ciki zuwa son ta yi wa jaririnta rauni.
“Lallai na ji a jikina cewa zan iya gwara kansa da bango, in jijjiga shi, in jefo shi daga saman bene. Kawai ji na yi ya lalata min rayuwa,” a cewarta.
A daidai wannan lokaci, an gano cewa Elaine tana fama da cutar tsananin damuwa bayan haihuwa kuma duk da cewa tana shan magunguna, amma ba ta jin dadin jikinta kuma tana nuna ba matsala.
Ta bayyana cewa a lokaci guda sai tunanin mai kyau ya shigo mata sai ta ajiye jaririn a kan gadonsa sannan ta nemi taimako.
Mai fafutuka Dakta Smith ya ce: “A Amurka da Canada suna da shirye-shirye dake rage yawan samun rauni a kai, amma mu a nan babu abin da muke yi kuma akwai bukatar sauyi.
“Sakonmu daya ne. Sai a ce kukan jariri ba wani abu bane, za su daina kuma ba wani abu bane don ka ajiye jaririn na dan lokaci muddin jaririn na wuri mai tsrao.”