-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Jihohin Najeriya Da Za A Yi Karon Batta A Zaben Gwamna


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Zaben gwamnoni a Najeriya na daukar hankali saboda tasirinsu a siyasar kasar.

A ranar Asabar ne al’ummar Najeriya za su koma rumfunan zabe domin zaben gwamnoni da ‘yan majalisar jiha bayan kammala zaben shugaban kasa.

A yanzu haka abin da ‘yan kasar suka zura ido su gani shi ne irin gumuruzun da za a yi a zaben na gwamna a ranar Asabar.

Akwai jihohi kalilan da tuni aka yi hasashen ‘yan takarar da za su lashe zaben jihohin sakamakon karancin karfin jam’iyyun adawa.

A wasu jihohin kuma, kamar mace ce mai ciki, ba a san abin da za ta haifa ba, saboda girman adawa tsakanin ‘yan takara a jihohin inda da wuya a iya hasashen wanda zai iya lashe zaben gwamna a jihohin.

Jihohin da ake ganin zaben gwamna zai fi zafi sun hada da :

Jihar Kano

BBC

Kamar yadda ake yi wa kallon siyasar Kano sai dan Kano kuma ‘Kano ta dabo tumbin Giwa, ko da me ka zo an fika,’ hakan ya sa ake ganin zaben gwamna a 2019 a Kano zai fi zafi fiye da sauran jihohin.

Za a fafata ne tsakanin gwamna mai ci da ke neman tazarce Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC da kuma dan takarar Kwankwasiyya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP.

Ana ganin zaben gwamna Kano, fafatawa ce tsakanin tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon mataimakinsa gwamna Ganduje wadanda suka yi shekara takwas a gwamnati.

Manyan ‘yan siyasar na Kano ba sa ga-maciji da juna tun bayan zaben shekarar 2015, inda tsohon Gwamnan na Kano Kwankwaso ya goyi bayan mataimakinsa Ganduje.

Mutanen biyu sun shafe shekaru suna tafiya tare a siyasance kafin su raba-gari, inda Kwankwaso ya sauya sheka zuwa tsohuwar jam’iyyar da ya fito PDP daga APC mai mulki a yanzu.

Kalubalen PDP a Kano

Ana ganin yanzu babban burin Kwankwaso shi ne kayar da Ganduje a zaben gwamna, inda ya dora surukinsa a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP.

Wasu daga cikin jama’ar Kano na ganin zaben Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar kamar sake zaben Kwankwaso ne a kan mulki, domin kuwa ana zargin Kwankwaso ne zai ci gaba da jan akalar siyasar jihar.

Sai dai kuma rushe zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP da Kotun tarayya ta yi a jihar Kano wanda ya bai wa Abba Kabir Yusuf damar zama dan takarar gwamna a jam’iyyar babban kalubale ne ga aniyar Kwankwaso na kayar da tsohon mataimakinsa.

Amma Hukumar zabe a Najeriya INEC ta ce jam’iyyar PDP mai adawa tana da dan takarar gwamna a jihar Kano a matakin hukumar.

Sai dai ba a san me zai faru ba – Abba ne zai yi takara a PDP ko Ali Amin-Little da ke kalubalantarsa? Lokaci ne kadai zai iya tabbatar da haka.

Haka kuma yadda APC ta lashe dukkanin kujerun ‘yan majalisar tarayya wasu na ganin wani koma-baya ne ga makomar jam’iyyar PDP a zaben gwamna da za a yi a jihar.

Wannan zai iya sanyaya guiwar ‘yan jam’iyyar ta PDP a jihar fitowa zaben gwamna domin tunanin ko sun fito babu wani sauyi da za su iya samu.

Yadda wasu jiga-jigan PDP suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki ana ganin babban matsala ce ga tafiyar Kwankwasiyya.

Sannan kada jam’iyyar da ke mulki babban aiki ni ga jam’iyyar adawa ta PDP, duk da cewa siyasar Kano komi na iya faruwa, ba sabon abu ba ne kayar da gwamnati mai ci domin ta taba faruwa da Kwankwaso lokacin da yana gwamna wa’adinsa na farko.

A zaben 2003, Rabiu Musa Kwankwaso yana kan mulki Malam Ibrahim Shekarau ya kayar shi.

Amma a zaben 2011 Kwankwaso ya kayar da dan takarar gwamnati zamanin mulkin Shekarau a Kano.

Kalubalen APC a Kano

Gwamna Ganduje na jam’iyyar APC zai iya fuskantar kalubale a zaben 2019 diba da tarihin siyasar Kano.

Duk da Sanata Rabiu Kwankwaso ba ya da gwamnati amma tasirinsa a siyasar Kano musamman dimbin magoya bayansa kan iya zama barazana ga makomar Ganduje

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

- Advertisement -

Masharhanta na ganin wani al’amari da ake ganin zai yi tasiri ga masu kada kuri’a, shi ne zarge-zargen da ake yi wa Ganduje na wani bidiyo da aka bankwado wanda ya nuna gwamnan na karbar damman daloli.

Zargin rashawa da ake yi wa gwamnan APC a Kano wasu na ganin ya kara rage wa jam’iyyar Gandujei farin jini musamman a gwamnatin Buhari da ke da’awar yaki da rashawa.

Jihar Kaduna

BBC

Jihar Kaduna na cikin jihohin da ake ganin zaben gwamna zai ja hankali musamman tsakanin ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasa wato APC da kuma PDP.

Gwamnan Kaduna Malam El-Rufai dan takarar APC zai fafata ne da babban mai hamayya da shi Isah Ashiru Kudan na jam’iyyar PDP.

Zaben gwamna a Kaduna zai kara daukar hankali ne ganin yadda gwamna El-Rufa’i ke takun-saka da wasu jiga-jigan jam’iyyarsa ta APC da ya tilastawa sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu.

Ana ganin yawancinsu suna adawa ne da gwamnan bayan hana su koma ga kujerunsu na majalisar tayya a zaben fitar da ‘yan takarar APC.

‘Yan siyasar sun hada da Sanata Suleiman Othman Hunkuyi wanda ya koma jam’iyyar PDP da kuma Sanata Shehu Sani wanda ya koma jam’iyyar PRP.

Sai dai masharhanta siyasa na ganin wadannan ‘yan siyasar ba su yi wani tasiri ba, bayan sun sha kaye a zaben ‘yan majalisa da aka gudanar tare da na shugaban kasa.

Amma siyasar kabilanci na iya yin tasiri ga zaben gwamna a Kaduna a 2019, ganin yadda zaben shugaban kasa ya raba jihar gida biyu inda kudancin Kaduna suka zabi jam’iyyar PDP mai hamayya, arewacin Kaduna kuma suka zabi jam’iyya mai mulki APC.

Batun daukar musulma a matsayin mataimakiyar gwamna El-Rufai ya janyo ce-ce-ku-ce tare da kara haifar da zafin siyasar kabilanci a Kaduna.

Ana ganin zaben 2019 zai raba mabiya addinin musulunci da Kirista ia Kaduna inda ake ganin Musulmai za su zabi Malam Nasiru el-Rufa’i na APC yayin da kuma bangaren Kiristoci kuma za su zabi dan takarar PDP Isa Ashiru saboda ya dauki Kirista a matsayin mataimaki.

Jihar Gombe

BBC

Gombe na daga cikin jihohin da ake ganin za su ja hankali a zaben gwamna.

Jam’iyyar APC mai adawa za ta yi kokarin kwace mulki ne daga hannun jam’iyyar PDP da ke mulka a jihar.

Za a fafata ne tsakanin Usman Bayero Nafada na jam’iyyar PDP da kuma dan takarar jam’iyyar APC Inuwa Yahaya

Ana ganin zaben Gombe fafatawa ce tsakanin gwamnan jihar mai barin gado Ibrahim Hassan Dankwambo da kuma tsohon gwamnan jihar kuma uban jam’iyyar APC Danjuma Goje.

Ganin yadda gwamna Dankwambo ya kasa lashe kujerar majalisar dattawa, wasu na ganin babban kalubale ne ga jam’iyyarsa ta PDP da ke mulki a zaben gwamna.

Jihar Sokoto

BBC

Siyasar jihar Sokoto ta yi matukar bayar da mamaki musamman a zaben shugaban kasa da aka gudanar ganin yadda jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ta samu kuri’u masu yawa.

A bara ne gwamnan jihar ta Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya sauya sheka daga APC zuwa PDP domin takarar shugaban kasa inda bai samu nasara ba.

Tambuwal na neman tazarce ne a wa’adi na biyu inda zai yi takara tare da tsohon mataimakinsa Ahmed Aliyu wanda APC ta tsayar dan takararta kuma wanda tsohon gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamakko ke marawa baya.

Yadda ake muhawara sakkoto

Yakin lashe zabe zai kasance ne tsakanin gwamna Tambuwal da ke samun goyon bayan tsohon gwamna Attahiru Bafarawa da kuma Magatakarda Wamakko da ke yakin ganin dan takararsa ya ci zabe.

Wasu na kallon siyasar Sakkwato a bana kamar yaki ne na kawo karshen siyasar uban-gida.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: