Jihar Akwai Ibom Ta Kashe Naira Biliyan Biyar Don Gyara Fannin Lafiya!

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

- Advertisement -

Ina Kuke Gwamnonin Arewa ?

Daga Abdullahi Muhammad Maiyama

Wani abun mamaki shine yadda gwamnatin jihar Akwa
Ibom ta kashe zunzurutun kudi har naira Biliyan biyar
don inganta Asibitocin jahar.

Babban abunda ke daure mun kai shine akwai Asibitoci a jahar ta Akwa Ibom wadanda Gwamnatin PDP ta fara, amma hawan wannan
gwamna duk ya kammala su.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 27

Amma gashi a Arewacin
Nijeriya ana fama da matsalar cinkoson jama’a
musamman a asibitocin mu na cikin gida, ga karancin kayan aiki da rashin magunguna.

Jihar Akwa Ibom jiha ce da take da karamcin jama’a idan akwai kwatanta da wasu jahohin arewacin najeriya, amma abun ban takaici kaf Arewa baka tabajin wata jaha ta ware koda biliyan uku ne don inganta Asibitoci kawai ba.

Lallai kalubale ne ga gwamnonin Arewacin Nijeriya. Lokaci ya riga ya zo da ya kamata ku tashi tsaye wurin kawowa jama’ar da kuke
mulki dauki, musamman a daidai wannan lokaci da
sabbin cututtuka ke bullowa wadanda idan ba a kula ba
sai sun yi lahani sosai.

Allah dai ya kawo muna agaji.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.