Labarai

Jigawa: Dalibai 'sun kashe abokinsu don zargin luwadi'

‘Yan sandan jihar Jigawa da ke arewacin Nigeria, sun cafke dalibai 15 da ake zargi da hannu a kisan abokinsu a kwalejin gwamnati da ke karamar hukumar ‘Yankwashi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Jinjiri Abdu, ya tabbatarwa BBC faruwar lamarin.
Mista Jinjiri ya kara da cewa daliban da aka kama ‘yan makarantar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta gwamnati ce da ke karamar hukumar Karkarna, an kama su ne a ranar 8 ga watan nan.
 
Ya kara da cewa daliban na tsakanin shekara 17 zuwa 19, an yi zargin dukan da suka lakadawa abokin nasu ne ya yi ajalinsa.
Sannan suka dauki gawar mamacin, suka jefar da ita a wani daji da ke kusa da makarantar a ranar 6 ga watan Agustar nan, da misalin karfe 2 da rabi na dare.
”Wadanda ake zargin sun kafa wani kwamitin ladabtar da mamacin, bayan sun yi zargin wai dan luwadi ne.”
“Da safiyar wannan ranar suka yanke shawarar abin da za su yi suka dauke shi cikin daji, kana suka lakada masa duka da sanduna.”
“Bayan sun gama dukansa, sai suka dauko gawar tare da jefar da ita a dajin, sai da safe sannan hukumomin makarantar suka ga gawar,” in ji Mista Jinjiri.
Jinjiri ya ce a asibiti ne likitoci suka tabbatar da mutuwarsa, jami’an tsaro na ci gaba da bincike kan lamarin.
Nan ba da jimawa ba, za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban shari’a.
Tuni iyayen mamacin suka karbi gawarsa an kuma yi masa sutura.
A kwanakin baya ne hukumomin tsaro na ‘yan sanda da Civil Defence suka kama wasu dalibai hudu suma ‘yan wannan makarantar, da laifin sace kwamfiyutar hannu samfurin Samsung.
Daga bisani aka gano daliban sun sace kwamfiyutar ne, daga dakin adana kwamfiyuta na makarantar.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.