Da alama dai dokar bayarda lada ga duk wanda ya yi tonan silili game da cin hanci da rashawa tana cimma ruwa, inda a yanzu haka hukumar EFCC ta sake samo motoci zunduma zunduma har guda 17 a gidan wani tsohon shugaban kwastam mai suna Abdullahi Dikko Inde a Kaduna.
Hukumar ta iya gano hakan ne bayan da wani ya tsagunta mata cewa akwai yiwuwar an ajiye kudaden sata da kadarori a wani gida da ke kan titin Nnamdi Azikiwe a jahar.
Jami’an hukumar reshen Kano sun garzaya zuwa gidan, inda bayan sun kammala binciken su, suka yi awan gaba da motoci guda 17.
Haka kuma sun tafi da mutane biyu da suka samu a gidan, wadanda ke da alhakin kula da kadarorin.
Ga jerin motocin kamar yadda aka samu:
i. Bakar BMW kirar 525i 2010
ii. Hyundai kirar Velester 2012, ruwan toka
iii. Shudiyar BMW 325i, 2003
iv. Bakar Land Cruiser Prado Jeep, 2014
v. Bakar Mercedes G wagon, 2013
vi. Bakar BMW 335i series, 2012
vii. Peugeot 406, 2002 ruwan silva
viii. Bakar Land Cruiser Prado Jeep, 2014
ix. Toyota FJ Jeep, 2007 ruwan dorawa
x. Bakar Toyota Avensis, 2013
xi. KIA Cadenza, 2011 ruwan toka
xii Porsche Cayene, 2009 model ruwan silva
xiii. Honda Accord, 2013 ruwan gwal,
xiv. Farar Nissan Urban Bus, 2006
xv. Farar Nissan Urban Bus, 1996
xvi. Farar Toyota Hiace Bus, 2010
xvii. Farar Nissan Bus, 2009

Daure
Add Comment