Kimiyya

Jawabin Sheik Isah Ali Fantami Kan Fasahar Zamani

Tsarin Da Zai Taimakawa Fasahar Zamani Da Ceto Makudan Kudi Da Ake Kashewa Wajen Shigo Da Kayyakin Fasaha Daga Kasashen Ketare

Dokta Isa Ali Ibrahim Pantami (FBCS), shugaban hukumar bunkasa fasahar zamani ta kasa (NITDA) ya kawo tsari guda bakwai wanda hukumar sa take kokarin samar da su.

Sanya ido akan yanda ake aiki da fasahar zamani da tsoratar wa akan dokoki bisa ga yanda hukuma ta bawa ma’aikatar dama ta tsoratar.

 

Tsarin taimaka wa wajen ciyar da gaba domin takaita aiki da takarda a gwamnatance dan komawa ga komfuta.

Taimakawa domin amfani da fasahar gida ta hanyar kamfanoni da mutane masu harkar komfuta ta yanda za’a taimake su da kara musu fasaha, da wayar da kai ga hukumomin gwamnati da suna aiki da abun da akeyi a gida saboda takaita kashe kudi a kasashen waje.

Samar da Sana’oi wa matasa da sauran mutane kamar mata da yara sana’o’in da shafi aiki da komfuta.

Taimakawa ma’aikata domin kara habbaka ilmin su domin tafiyar da tsarin gwamnati acikin na’ura mai kwakwalwa.

Tsarin kula da tsaro na komfuta.

Taimakawa fasahar gida wato kamfanonin gida, da aiki da ilmin matasa da suke da fasahar zamani domin rage amfani da abubuwan waje, kamar yanda fadar shugaban kasa ta bada umurni duk wani bangaren gwamnati da zasuyi aiki da fasahar zamani da suyi aiki da kashi 40 cikin 100 na fasahar cikin gida, kuma akwai bangaren tallafawa masu kwazo a wannan bangare.

Gwamnati tana iya kokarinta na fadada hanyoyin dogaro ga tattalin arziki ta hanyar bunkasa fasahar zamani domin fasahar zamani ita take jagorantar tattalin arziki a kowani bangare a duniya, shi ya sa Darakta Janar na NITDA DR. ISA PANTAMI yake iya kokarin sa wajen cimma manufar wannan ma’aikata na fasaha ta zamani.

 

‘Source In Jaridar Rariya’

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.