Kannywood

Jarumi Nuhu Abdullahi Ya Shiga Duhu – Ko Menene Matsalar?

Jarumi Nuhu Abdullahi yana daga sahun jarumai masu tasowa akannywood. kuma jarumine wanda yake da kwazo wajen gudanar da aikin fim. yana taka muhimmiyar rawa acikin fim din ‘FURUCI’, wanda ya fito amatsayin dan tasha mara mutunci.

Sannan Nuhu Abdullahi ya shirya fina finai na kan shi. haka kuma ya fito acikin manyan fina finan turanchi kamar haka: There Is A Way, The Light And Darkness, Thorny. duk wanda tashe da Nuhu Abdullahi ya yi, duk ashekarar 2015/2016.

 

Anyi zaton tauraruwarsa zata ci gaba da haskawa a 2017/2018, amma abin mamaki sai ga shi ya shiga duhu. nema akeyi amanta da shi aduniyar kannywood. ko menene yasa aka jima ba’a fuskar shi ba acikin sababbin fina finan wannan shekara?
Karatun da jarumin yaci gaba da yi, yana daya daga dalilan da suka sa ya shiga duhu kamar yanda ya sanarwa jaridar Premium Time. Acewarsa: Na koma makarantane dan haka naja da baya dayin fim. amma har yanzu ina fitowa a fim ba dainawa nayi ba.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.