Kannywood

Jarumar Kannywood Aisha Tsamiya Tasha ruwan Duwatsu, Ko mene ya janyo haka?

Shahararriyar jarumar nan ta wasan Hausa watau Aisha Aliyu wadda akafi sani da Aisha Tsamiya mun samu labarin cewa ta sha ruwan duwatsu a garin Kano da sallar da ta gabata.

Majiyar mu dai ta ruwaito cewa wasu mafusatan samari ne suka yi wannan aika-aika a lokacin da ake shagulgulan sallar da ta gabata a filin kasuwar baje koli dake a jihar ta Kano.

Arewablog sun  samu labarin cewa mahalarta taron sun huce haushin su ne akan Tsamiya sakamakon makara da ta yi zuwa wajen taron, wanda hakan ya sa su yi mata ihu gami da ruwan duwatsu har ta kai sai da kyar jami’an tsaro suka kwace ta.

A baya ma dai jaruma Nafisa Abdullahi ta sha da kyar a jihar Katsina inda magoya bayan ta da masoya suka yi mata ca sai da kyar aka samu aka kwace ta sadda tazo yin wani wasa kafin azumi.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.