Kannywood

Jarumar Finafinan Hausa, Hafsat Barauniya Ta Aurar Da ‘Yarta Ta Uku

DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO, Mujallar Film
Tauraruwar finafinan Hausa Hafsat Idris ta aurar da ɗiyar ta ta uku a ƙarshen gagarumin bikin da aka ɗau kwanaki ana yi a birnin Kano.

Hafsat, wadda ake yi wa laƙabi da ‘Ɓarauniya’, ta aurar da Khadija Kabir ne ga wani matashi mai suna Abubakar Ibrahim Muhammad.

An auren da misalin ƙarfe 12:00 na rana a unguwar Ɗandago cikin ƙwaryar Kano a kan sadaki N50,000.

Taron ɗaurin auren ya samu halartar ɗimbin ‘yan’uwa da abokan arziki, amma mujallar Fim ba ta ga fuskar abokan sana’ar uwar amarya a wurin ba.

To sai dai sun yi mata kara a sauran shagulgulan da aka gudanar, ciki har da liyafar cin abincin dare da aka yi a ranar Juma’a, 26 ga Maris, 2021 a wurin taro na Fabs dake Kano.

Ɗimbin ‘yan’uwa da abokan arziki sun halarci dinar, ciki har da ‘yan fim da mawaƙa irin su Ali Nuhu, Nazifi Asnanic, Lawan Ahmad, Hamisu Breaker Ɗorayi, Teema makamashi, Ruƙayya Dawayya, Saratu Giɗaɗo, Halima Atete, Samira Ahmad, Fatima Ali Nuhu, Ummi Rahab, Aisha Humaira, da sauran su.

Tun a yammacin ranar Alhamis din da ta gabata ne aka gudanar da kamu a Ezema Events Centre, taron da shi ma ‘yan’uwa da abokan arziki da dama su ka halarta.

Amarya Khadija Kabir dai ita ce ta uku a cikin jerin ‘ya’yan Hafsat Idris guda shida waɗanda su ka haɗa da maza biyu mata huɗu.

Bikin auren ya yi armashi, an ba naira kashi, sai dai mu ce Allah Ya ba da zaman lafiya da ƙazantar ɗaki, amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: