Kannywood

Jaruman Kannywood Maza Da Suka Haska a 2016

A ‘yan kwanakin da suka gabata ne muka kawo muku jerin sunayen jarumai mata da suka fi haskawa a shekarar nan ta 2016.
A yau kuma muna tafe da jerin jarumai maza.
Mubarak Umar na Jaridar Leadership Hausa ya yi nazari na musamman ta hanyar duba da rawar da kowanne jarumi ya taka a finafinan da suka fito a 2016 a kowanne bangare da suka hada da jarumta, barkwanci da sauransu.
A yi karatu lafiya.
1- Sadiq Sani Sadiq
sadeeq-sani
Wannan jarumi cikin ‘yan shekaru yana taka rawar da yake tserawa tsara a tsakanin takwarorinsa, musamman yadda yake iya juya kansa zuwa siffofi daban-daban a cikin finafinai.
Matsayin da ya fito a Kurma cikin shirin DAN KURMA ya kayatar matuka. Yadda yake magana tamkar wanda ya yi a karatu a makarantar kurame, lamarin akwai ban mamaki. Kullum jarumin yana kokarin ganin ya zo da wani sabon abu wanda masoyansa ba su saba gani ba.
Dan Kurma shiri ne na barkwanci, wanda Sadik suka fito tare da jaruma Hafsa Idris (Barauniya). Masu sha’awar kallon finafinan Hausa musamman na barkwanci sun yaba sosai da rawar da jarumin ya taka.
A kullum yaumin jarumi Sadik na amfani da wani irin tunani wajen zabawa kansa rol din da zai fito a ciki. Ba ya duba tsadar kudin da za a ba shi, illa iyaka wane matsayi zai fito.
Wannan na daga cikin manyan dalilin da suka sanya a ‘yan shekarun nan jarumin yake lashe manyan kyautuka a yayin gudanar da gasar karrama jaruman Kannywood
2- Nuhu Abdullahi
nuhu-abdullahe
Babu shakka yanayin da jarumin ya fito a cikin Fim din FURUCI ya gamsar da kaso 90 cikin 100 na mutanen da suka yi sharhi a kai. Hakika Nuhu ya nunawa duniya cewar lallai ya kawo karfi da zai iya yin gogayya da manyan jaruman Kannywood. Yadda ya bayyana a matsayin dan tasha, ba shi da tsoro, duk abin da zai da karfin zuciya yake aikata shi. Yayin da mutum yake kallo, yana iya mancewa fim ne ko kuma gaske.
Bayan nasarar da ya samu na shiga sahun jaruman da ake labarinsu sakamakon rawar da ya taka a fim din Furuci, Nuhu Abdullahi ya fara haskakawa a finafinan Turanci, wanda labaransa ke da alaka da zamantakewar rayuwar Hausawa.
Finafinan Turanci guda uku da ya fito a ciki, THERE IS A WAY, LIGHT AND DARKNESS da kuma THORNY, sun kara tabbatar da cewar shekarar 2016 ta zo wa jaruman da babbar nasara, ta yadda ba zai iya mantawa da ita ba.
3- Isah Adam
isah-adam
Jarumin BASAJA GIDAN YARI, wanda bayyanarsa ta sauya yanayin shirin baki dayansa, ya samu nasarar darewa sahu na uku sakamakon rawar da ya taka a cikin wannan shiri.
Yanayin da ya fito na babu sani babu sabo a tsakiyar manyan jarumai ya birge manazarta matuka. Zuwa yanzu za a iya cewa jarumin bai taba taka rawa irin ta Basaja Gidan Yari ba.
Fitowarsa ta kara daga kima da darajar fim din, musamman da ake ganin sa matashi, kyakkyawan jarumi mai cikar zati. Idan har Isah ya ci gaba da taka rawa irin wadda ya yi a Basaja, babu shakka nan da ‘yan wasu kwanaki zai shiga sahun manyan jarumai da ake labarin su a Nijeriya.
4- Ali Nuhu
ali-nuhu-2
Sarki Ali, kamar yadda masoyansa suka yi masa lakabi, ba ya bukatar dogon bayani game da yadda yake jan zarensa a masana’antar shirya finafinan Hausa, watau Kannywood. Gwani ne da aka hakikance cewar batu na aktin a jikinsa kullum karuwa yake yi.
Rawar da ya taka a fim din UMAR SANDA,wanda darakta Kamal S. Alkali ya bada umarni, ya zo da wani irin salo da ya birge ‘yan kallo. Bayyanar damuwa a fuskar Ali Nuhu a cikin shirin, da kuma yadda ya kasance namijin duniya mai yadda da kaddara a duk lokacin da wata musiba ta fadawa mutum. Nuhu ya kara tabbatar wa da duniyar finafinai shi din kwararre ne da kwanyarsa take ja.
Wani masani da ya yi sharhi kan fim din ta wayar tarho ya ce, “Akwai bukatar duk dan Nijeriya musamman jami’an tsaro su kalli fim din Umar Sanda, domin cike yake da sako mai matukar ma’ana.
5- Adam A Zango
adamu-zango
Tabbas rawar da Jabir (Adam A. Zango) ya taka a shirin Basaja GIDAN YARI abin yabawa ce, domin idan kana son gane wane ne Zango a fagen aktin, to ka kalli Basaja. A ciki ne yake nunawa duniya cewar shi din cikakken jarumi ne da duk masana’antar da ya kasance a cikinta za ta yi alfahari da shi.
Zango yana amfani da kwarewa matuka musamman a yayin da yake magana ko motsi a cikin fim din Basaja. Ko idonsa ya motsa, dan kallo yana iya gano me yake shirin faruwa ko kuma abinda yake nufi. Hakan na kasantuwa saboda nakaltar labarin da ya yi tamkar a gaske abin yake faruwa.
Haka zalika fim din MIJIN BIZA da ya fito a matsayin matashin mayaudari, ya dace da rol din matuka. Kayan da yake sanyawa, tafiyarsa da maganarsa sun fassara wane ne shi. Motsin jikinsa kawai abin yabawa ne.
6- Rabi’u Rikadawa
rabiu-rikadawa
Zakulo fim guda a yi magana a kansa zai yi matukar wahala, domin Rikadawa jarumi ne cikakke da ya kware wajen sarrafa basirarsa ta fuskoki da dama.
Jarumi ne da ba ya shakkar karbar rol kowane iri ne, ya iya taka rawa kala-kala domin birge ‘yan kallo. Gwani ne da hatta turawan BBC sun sallama masa  a fagen aktin.
A cikin fim din Zinaru an ga yadda ya fito a dan wiwi, kai ka rantse da ma can yana sha. Yanayin tafiyarsa, maganarsa da motsinsa ya yi matukar dacewa da yadda ‘yan wiwi suke yi.
7- Yakubu Muhammad
yakubu-mohammed-kannywood
Fim din Turanci mai suna SONS OF THE CALIPHATE, na cikin jerin finafinan Yakubu ba zai manta da su ba a rayuwarsa ta duniyar nishadi. Duk da cewar shirin an yi shi ne da harshen Turanci, amma hakan bai hana Fim din mamaya a Arewacin Nijeriya ba.
Yakubu Muhammad ya fito a dan gidan attajiri, wanda ba ya shakkar murza Naira a kasa. Rawar da ya taka ce ta sanya shi zamowa cikin wannan jeri a matsa yin na bakwai.
Kasancewar fim din Sons of the Caliphate yana bada labarin yadda ‘ya’yan masu fada a ji ke tafiyar da rayuwarsu musamman a Arewaci, ya sanya aka zakulo jarumai irin su Yakubu daga Arewa. Labarin kacokan kan yanayin rayuwar ‘ya’yan sarakuna ne da masu hannun da shuni.
Zubin tsarin shirin na rayuwar Hausawa ne da yanayin shugabancinsu, bambancin guda daya tak kawai da aka yi shirin da harshen Turanci.
8- Sulaiman Bosho
bosho
Idan ana batun finafinan ban dariya a masana’antar finafinan Hausa a yanzu babu kamar sa. Duk ta inda aka bullo sai ya bulle domin ya nishadantar da ‘yan kallo.
Fim din HEDIMASTA da Sulaiman Bosho ya fito a matsayin Shugaban Makarantar furamare ya bawa mutane dariya matuka. Yadda ya fito a jahilin malamin makaranta, bai san bihim ba, ko wani abu da ya danganci ilmin boko, amma ya yi kane-kane tamkar wani farfesa a jami’a.
Salon barkwancin da ya fito da shi ya rage wa masoya kallon finafinan Hausa radadin rasuwar Rabilu Musa Ibro shekaru biyu da suka gabata.
Bosho ya taka rawa a shirin Hedimasta, ya nishdantar da masu sha’awar kallon finafinan Barkwanci da harshen Hausa matuka.
9- Ramadan Booth
ramadan
Rawar da ya taka a cikin fim din SAPEENAH, wanda babban darakta Sunusi Oscar 442 ya bada umarni, ta shiga sahun tarihin jarumin. Hakika Ramadan ya yi amfani da kwarewa matuka wajen nuna kansa a fagen aktin.
Har ila yau, GWARZON SHEKARA, fim ne da yake bada labarin yadda wani matashi (Ramadan) ya kamu da tsananin son jarumin fim, watau Ali Nuhu. Ya kasance ba ya bibiyar komai in ba labarin jarumin ba, inda yake wasa da duk wani abu da ya shafe shi.
Ramadan ya taka rawa da za ta birge mutane a cikin wannan fim, domin ya fito ne da wata irin fuska da ba taba ganisa ba. Duk da cewa fim din bai fita kasuwa ba, amma manazarta sun zuba ido domin ganin yadda za wanye ta cikin wannan shiri.
10- Abdul M. Shareef
abdul-m-shariff
Tallar fim din JANI MU JE kadai da ta fita a shekarar nan ta rikita masu kallon finafinan Hausa. Rawar da jarumin ya taka ta gwarzon namiji, da ya tsinci kansa a tsakiyar abokan gaba, mugaye da suke yunkurin zaluntar wata budurwa.
Abdul ya yi amfani da matakin karfin tuwo wajen kwato yarinyar daga hannun Basawa. Yanayin yadda yake tayar da kwanji tamkar wani dan dambe akwai kayatarwa matuka.
Yana cikin jaruman da ake yi masu kyakkyawan fatan nan da ‘yan wasu kwanaki zai shiga sahun wadanda ake damawa da su

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.