-Advertisement-


Jaruma Amal Umar Za Tai Aure A Karshen Wannan Watan


2 839

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

– Wata majiya kwakwara ta tabbatar da cewa matashiyar jaruma Amal Umar, zata zama amarya a ranar 27 ga watan Janairu
– Majiyar ta tabbatar da cewa dukkan shirye-shirye da ya danganci bikin auren jarumar ya kammala amma ta boye ne har sai ana gab ta sanar
– Kamar yadda bincike ya nuna, jarumar zata auri wani fitaccen dan kwallon kafa ne don sun dade suna soyayya dashi

-Advertisement-

-Advertisement-

Sananniya kuma fitacciyar matashiyar jaruma, Amal Umar za ta yi aure a wannan watan na Janairu 2020, in ji wata kwakwarar majiya da ta sanar wa mujallar Fim.

Majiyar, wadda ke da kusanci da jarumar, ta tabbatar mana da cewa duk wani shiri na bikin ya kammala.

“An fitar da ranar 27 ga watan janairu don daura auren Amal tare da wani saurayi da ta dade tana soyayya dashi,” cewar majiyar.

Da yake Amal tana nuku-nuku da maganar auren nata, kokarin mujallar Fim tayi magana da ita ya gagara. Wakilin mujallar fim ya kira sau da yawa a waya amma ba a samunta.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 320

-Advertisement-

Hakazalika bata mayar da martanin sakon kar ta kwana da aka tura mata ba.

Idan zamu tuna, cikin kwanakin nan ne jarumar ta dawo daga aikin Umrah.

Tana daga cikin matasan ‘yam mata da suka shiga harkar fim din da kafar dama, domin cikin kankanin lokaci ta fito a manyan fina-finai da suka daga sunanta.

Da yake jarumar ta iya turanci, ta sake yin suna a wasu manyan fina-finan Kudancin Najeriya wato Nollywood.

#Hausalegit

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.