Labarai

Jarrabawar NECO Ta Nuwamba 2016 Ta Fito, Dalibai Mafi Rinjaye Sun Yi Nasara

Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Babban Sakandire Ta Kasa NECO ta saki sakamakon jarrabawar da ta ke shiryawa a watannin Nuwamba da Disamban kowace shekara ga masu neman gyara takardunsa da ake kira a turance GCE 
Shugaban hukumar, Farfesa Charles Uwakwe ya ce an saki jarrabawar ce kwanaki sittin cif da kammala zana jarrabawar wanda wannan sakamako shi ne ya fi kowane saurin fita tun da aka kafa hukumar
Dalibai 47,941 suka yi rijistar zana jarrabawar. Daga wannan adadi, dalibai 47,118 ne suka zauna jarrabawar inda dalibai 28,530 suka yi nasarar cin kwasa-kwasai biyar ciki har da turanci da lissafi wanda wannan adadi ya ke daidai da kaso 60.55 cikin 100 na wadanda suka zauna jarrabawar

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.