Labarai

JANAR ATTAHIRU: Gadanga Kusar Yaki An Kwanta Dama

Ina daga cikin ‘yan uwa Musulmi da muka yanke alaka da facebook na tsawon awanni 24 don hukunta Facebook akan goyon baya da take baiwa Isra’ila, amma mutuwar shugaban sojojin kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru itace ta sa na dawo.

Janar Ibrahim Attahiru yayi hatsari a jirgi a Kaduna ya mutu tare da wasu manyan hafsoshin sojin Nigeria kuma ‘yan Arewa Musulmi, hakika Arewa mun yi babban rashi.

Akwai bukatar ayi bincike sosai akan dalilin hatsarin jirgin, hatsarin jirgi a Nigeria bai cika rutsawa da mutanen banza ba, kuma ba’a cika fitar da bayanai akan dalilin hatsarin ba.

Janar Ibrahim Attahiru soja ne mai gaskiya da amana wanda yake da niyyar ya ga bayan karshen ta’addancin Boko Haram, kafin ya samu wannan mukamin, ya taba rike rundinar da take jan ragamar yaki da Boko Haram a Maiduguri, a lokacin ya ki ya bada hadin kai a yi rashin gaskiya, wannan dalilin ya sa suka cire shi da wuri.

Mun san me kananun sojoji da suke fagen daga suke fadi na alheri akan wannan bawan Allah, tabbas ya kamata a gudanar da bincike, kuma a sanar da duniya sakamakon bincike na abinda ya haddasa hatsarin jirgin.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya saka masa da Aljannah Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: