Jam`iyyarka Ta PDP Ba Zata iya Daukar Nauyin Yakin Zabenka Ba -APC Ta Yiwa Atiku Shagube

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Jam’iyyarka ta PDP ba zata iya daukar nauyin yakin zabenka ba – APC ta yiwa Atiku shagube

A jiya Talata ne jam’iyya mai mulki ta APC, da kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, suka yi musayar yawu kan yadda za a samu kudaden da tsohon mataimakin shugaban kasar zai gudanar da yakin zabensa da su.

A yayin da APC ke ikirarin cewa Atiku da jam’iyyarsa na fuskantar babbar barazana wajen tattara kudaden yakin zaben nasa, shi kuwa dan takarar shugaban kasar karkashin PDP ya ce ba za’ayi amfani da kudi wajen samun nasarar zaben 2019 ba.

Mataimakin sakataren watsa labarai na APC na kasa, Yekini Nabena, a cikin wata sanarwa daya rabawa manema labarai a Abuja, ya yi ikirarin cewa duba da irin tsauraran matakan da gwamnatin yanzu ta dauka, PDP na cikin mauyacin hali wajen daukar nauyin yakin zaben Atiku.

Nabena ya yi ikirarin cewa akwai bayanai da suka samu, da ke nuni da cewa yunkurin PDP na samun kudin yakin zaben daga jama’ar kasar yaci tura, yana mai cewa “Wannan karnin Buhari ne, karnin da ke bin diddigin shige da ficen kudade a kasar, ba wai kamar lokacin Jonathan bane, inda aka bude baitul malin kasar ga PDP don daukar nauyin yakin zaben tsohon shugaban kasar.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 662

“Don haka shuwagabannin jam’iyyar PDP na cikin wani mawuyancin hali, da tunanin yadda zasu samo kudaden da zasu daukin nauyin yakin zaben Atiku Abubakar.”

Nabena ya shawarci hukumomin kasar da ke yaki da cin hanci da rashawa da su tabbata sunbi diddigin kudaden da kowacce jam’iyyar siyasa ta kashe wajen daukar nauyin yakin zabenta.

Sai dai mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya yi fatali da wannan ikirari na Nabena, yana mai cewa zaben 2019 da ke gabatowa, ba wai zabe bane da za’ayi amfani da kudi, illa dai al’umma ce zata zabawa kanta shugaban da ya fi dacewa da ita.

Ya ce:”Ina da yakinin cewa ‘yan Nigeria za su zabi Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasarsu a watan Janairun 2019, duba da irin barnar da gwamnatin APC ta tafkaa kasar.”

#Mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: