A GOBE NE JAM’IYYAR PDP ZATA FARA ZAGAYEN QANANAN HUKUMOMI DON TALLATA DAN TAKARARTA NA Gwamna DA SAURAN ‘YAN TAKARKARU
Daga: Hussain Lawan Bello Abu-Leenah
Mai girma Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin tutar jam’iyyar PDP Engr. Abba K. Yusuf zai Fara zagayen kananan hukumomin jihar Kano 44 daga gobe alhamis 20/12/2018.
Kamar yadda wakilin mu na Jihar Kano ya bayyana mana cewar Za’a Fara wannan zagayen ne ta Karamar hukumar Bichi, Kunchi da Tsanyawa.
Idan baku manta ba tuni Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta baiwa Yan takarkari damar fara yakin neman zabukan kasar nan a zabukan 2019 dake tafe.
Zaa fara gabatar da babban zabukan kasar nan a ranar goma sha shida ga wata Fabarerun shekarar 2019 dake tafe.
Dafatan zaayi siyasa bada gababa