Siyasa

Jam’iyyar PDP ta kara wa Makarfi watanni 4

Jam’iyyar PDP ta kara wa tsohon gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Makarfi watanni 4 ya ci gaba da jagorancin jam’iyyar.

PDP ta sanar da haka ne bayan kammala taron da tayi yau a filin Eagle Square da ke Abuja.

Bayan haka kuma ta sanar da rusa kwamitin rikon jam’iyyar a jihohin Anambara, Kebbi, Adamawa, Barno, Kwara, Ogun, Osun da na jihar Legas.