Daga El-farouq jakada
Gwamnan Jahar kogi ya bayyana jam’iyyar su ta APC ɗaya tamkar goma wanda tayi ayyukan da babu jam’iyar data yisu a duk fadin Afrika.
Ya bayyana Hakane a jiya wajen taron rantsar da Komittin canyo ra’ayoyin jama’a akan jam’iyyar ta Apc daya gudana a jiyan.
Bello ya ƙara da cewa jam’iyyar tasu kaɗai ta kawo cigaban da saidai a kwaikwayi halin ta, matuƙar ana son cigaban koda bayan babu su.
“wannan ba yinmu bane duk zaɓen da ake gudanarwa a jahar kogi muke cinsa , inada tabbas ɗin zamu cigaba da cinsa matuƙar za’ayi”,. Inji shi
Kamar yanda jaridar the cables ta ruwaito gwamnan ya ayyana jam’iyyar da ga-ga-ra-badau a jerin sauran jam’iyun siyasar Kasar nan.