Labarai

Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga Da Dama A Yayin Musayar Wuta A Jihar Zamfara

…an kashe ‘yan sanda hudu a yayin artabun
Daga Ibrahim Da’u Mutuwa Dole
An kashe jami’an tsaro biyar, da suka hada da ‘yan sanda hudu da wani jami’in NSCDC a yayin musayar wuta da ‘yan bindiga a yankin Gora Namaye da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta bakin kakakinta SP Muhammad Shehu, ta sanar da cewa an fatattaki wasu ‘yan fashi da dama, wadanda suka tare babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto.

Ya ce yanzu hanya a bude take ga masu ababen hawa kuma an fatattaki ‘yan fashin da suka shirya kai hari ga masu ababen hawa.

“Rundunar‘ yan sanda ta jihar Zamfara ta yi nasarar dakile wani harin da yan fashi da makami suka shirya kaiwa hanyar Gusau zuwa Sokoto, kusa da Dogon Karfe a karamar hukumar Bakura.”

“Harin wanda aka shirya yi wa matafiya daga ababen da suke da hannu a ciki, jami’an ‘yan sanda da ke aikin kiyaye hanya sun kiyaye hanya daga duk wata mamaya daga masu aikata laifi.

“A karshen artabun da ya dauki tsawon awanni,‘ yan fashi da yawa sun samu munanan raunuka tare da wasu daga cikinsu da ake zaton sun tsere da raunin bindiga.

Duk da haka sun sami nasarar kwashe gawarwakin saboda yawansu wanda aka yi zaton kusan 200 ne.

“Hanyar yanzu a buɗe take ga masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar, Za’a karfafa sintirin a hanyar don kauce wa ci gaba da toshewar hanyar” inji shi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: