Labarai

Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa sun kama tsohon ministan lantarki, Injiniya Saleh Mamman. 

Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati sun kama tsohon ministan lantarki, Injiniya Saleh Mamman.

 

Majiyoyi sun ce EFCC ta kama Saleh Mamman ne tun da sanyin safiyar Laraba inda suke ci gaba da tsare da shi a shalkwatar hukumar da ke Abuja.

 

Sun ce kamen na da alaƙa da zargin almundahanar wasu kuɗaɗe kimanin naira biliyan 22.

 

Zuwa yanzu, ba a ji wani martani daga ministan ko wasu makusantansa ba.

 

Rahotanni sun ce ana zargin sa da haɗa baki da wasu jami’ai a ma’aikatar lantarki waɗanda ke kula da asusun ajiyar kuɗaɗen ayyuka a tashoshin lantarki na Mambilla da Zungeru, don karkatar da kuɗi naira biliyan 22, tare da rabawa a tsakanin su.