Jami’an Banga Na Unguwar Jan Bulo Dake Birnin Kano, Sun Yi Nasarar Cafke ‘Yan Fashi Dauke Da Bindiga

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Jami’an ‘yan banga dake kula da Unguwar Jan Bulo a Birnin Kano, sun yi nasarar cafke wasu ‘yan ta’adda dauke da bindiga da kuma wukake.

Kamar yadda mai magana da yawun ‘yan bangar na Unguwar Jan Bulo wato Kwamanda Farouk Ibrahim Muhammad, ya bayyanawa Wakilin Jaridar Rariya , cewa barayi dauke da bindiga da kuma wukake sun hari wata mota domin kwace ta sai dai ba su yi nasara ba, inda daga karshe suka hari wani dan A daidaita Sahu, suka kwace mashin dinsa, bayan sun yanke shi da wuka amma da yake Unguwar tana da ‘yan banga wanda suke sunturi domin tabbatar da tsaro a Unguwar tasu, shine suka yi sauri suka ankarar da dukkanin jami’an nasu inda cikin kankanin lokaci suka cafke dukkanin yan ta’addar.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 773

Wanda tuni suka damka su a hannunan jami’an ‘yan sanda domin fadada bincike.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: