Hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami’a wato JAMB ta bayyana cewa daga bana za ta cire damar baiwa dalibai zabar jami’o’in gwamnati biyu a kan fom dinsu da a kira da zabi na farko da zabi na biyu (1st and 2nd choices)
Hukumar ta ce duk dalibin da ya zabi jami’ar gwamnati, to, zabinsa na biyu dole ya zama jami’a mai zaman kanta
Hukumar ta sanar da hakan ne a shafunta na twitter a kokarinta na samar da bayanai ajin farko kan yadda za a gudanar da jarrabawar JAMB a bana
Add Comment