Izala ta raba kan mabiyanta

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Zaben 2019 a Najeriya ya raba hankalin ‘yan Izala bayan da wani bangare ya ce yana goyon bayan Buhari, wani bangaren kuma ya bayyana goyon bayan Atiku.

Shugaban Izala daya daga cikin manyan kungiyoyin addinin Islama a Najeriya ne ya yi kira ga mabiyan kungiyar su zabi Buhari.

Talla

Matakin dai ya samu karbuwa da suka da ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan Izala musamman a kafofin sada zumunta inda wasu suka yi maraba wasu kuma suka ce ra’ayinsa ne ba da yawunsu ba.

Martani na farko ya fito ne daga fitaccen malamin addinin Islama kuma jigo a kungiyar Izala, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, wanda ya shaida wa BBC cewa dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar zai zaba.

Sheikh Rigachikun ya ce zai zabi Atiku ne saboda ya fi taimakon addinin Musulunci da taimakon jama’a da kuma amfanar da mutanen kasa.

Talla

Matakin bangarorin biyu ya ja hankali a shafukan sada zumunta musamman shafin Facebook na BBC Hausa bayan wallafa labarin.

Ra'ayin mutane a Facebook

Shiekh Abdullahi Bala Lau wanda ya tabbatar wa da BBC da matakin kungiyar na goyon bayan Buhari, ya ce sun yanke shawarar ne bayan wani taro na kasa da suka gudanar.

Ya ce sun lura yadda ake fuskantar lokacin zabe mawuyaci, ya kamata a yi saitin al’ummar musulmi kan abin da ya kamata.

Wasu ‘Yan Izala dai sun karbi kiran shugaban kungiyar inda suka ce Buhari za su zaba.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86
Ra'ayin mutane a Facebook
Ra'ayin mutane a Facebook

Sai dai kuma wasu ‘yan Izala sun bayyana adawa da matakin inda suka ce Atiku ne zabinsu, kuma hakan ba zai sa su fita daga kungiyar ba.

Ra'ayin mutane a Facebook

Wasu kuma sun bayyana ra’ayin cewa bai dace kungiyar addini ta fito ta bayyana goyon bayanta ba ga wani dan takara ko jam’iyyar siyasa ba, illa su tsaya a matsayinsu na malaman addini su yi wa kasa addu’ar samun zaman lafiya.

Wasu kuma na ganin siyasa ra’ayi ce, kowa yana da ‘yancin ya zabi wanda yake ganin ya kwanta masa a rai tsakanin ‘yan takarar.

Ra'ayin mutane a Facebook

Da alama zaben 2019 zai fi na baya ta fuskar rabuwar kawunan al’umma da ke mara wa mabambantan ‘yan takara baya.

Wasu masu sharhi kan al’amura a kasar suna ganin hakan bai rasa nasaba da yadda duka manyan ‘yan takarar biyu suka fito daga yanki guda wato arewacin kasar.

#BBC HAUSA

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: