Izala Ta Goyi Bayan Zaman Mukabala Tsakanin Abduljabbar Da Malaman Kano

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’ah Wa Iƙamatus Sunnah ta Kasa ta fito fili inda ta bayyana goyon baya dangane da matakan da gwamnatin Kano ta ɗauka na daƙile fitinar da Abdul-Jabbar ke haddasawa tare da yaba zaman muƙabala da aka shirya tsakanin shi da Malaman Kano.

Shugaban Kungiyar na ƙasa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawarshi da manema labarai a garin Kaduna.

Imam Bala Lau ya kara da cewar matakin da gwamnatin Kano ta ɗauka abin a yaba ne, kuma zai taimaka wajen kawo karshen yaɗuwar irin wadannan miyagun maganganu a tsakanin Musulmi.

“Irin wannan mataki ne Gwamnatin Jihar Neja ta ɗauka akan wani Mutum da ya fito yana miyagun maganganu akan Sahabban Manzon Allah SAW inda aka ɗauki matakin da ya dace domin samun zaman lafiya.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 747

Dangane da halin da tsaro ya shiga ciki musamman a yankin Arewacin Najeriya, Imam Bala Lau ya ce tuni Ƙungiyar Izala ta yi nisa wajen gudanar da da’awa da wa’azuzzuka a dazuka da rugagen Fulani a wasu Jihohin Arewacin Najeriya, jihohi irin su Adamawa, Katsina, Zamfara da Kebbi, domin Ilimantar da Fulani hasken ilimin addini, wanda Malaman Ƙungiyar ke gabatarwa cikin harshen Fulantaci.

Inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sa himma wajen sake farfaɗo da ilimin ‘ya’yan Makiyaya, domin kawar da jahilci a tsakanin su, kasancewar Jahilci ne ƙashin bayan dukkanin wasu fitintinu dake faruwa a ƙasar.

Imam Abdullahi Bala Lau ya kuma yaba kokarin da Dr. Ahmad Gumi ke yi na shiga cikin dazuka da ganawa da ‘yan bindiga domin samar da sulhu, inda ya ce wannan mataki ne mai kyau, amma Ilimantar da su wani muhimmin abu ne, muddin aka samu ilimi babu shakka ta’addanci zai kau, amma idan ya zamana babu ilimi ko da an yi sulhu da ‘yan bindiga suna iya sake komawa cikin fitina.

Shugaban na Izala ya kuma yi kira ga dukkanin jama’ar Najeriya da su dage wajen yin addu’o’i ga Allah SWA domin samun zaman lafiya a Najeriya da kawar da dukkanin wasu matsaloli da ke addabar ƙasar.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: