Wasanni

Italiya Ta Lashe Kofin Euro 2021 Bayan Doke Ingila a Bugun Fenariti

Kafin wasan ya je ga matakin bugun fenaritin, Ingila ce ta fara sammakon zura kwallo a ragar Italiya, abin da ya ba ta damar mallake wasan gabanin a je hutun rabin lokaci.

Wasan ya kai matakin fenaritin ne bayan da kasashen biyu suka yi kunnen doki da ci 1-1, lamarin da ya sa aka kara lokaci kafin a je ga bugun daga kai-sai-mai tsaron-gida.

Kafin wasan ya je ga matakin bugun fenaritin, Ingila ce ta fara sammakon zura kwallo a ragar Italiya, abin da ya ba ta damar mallake wasan gabanin a je hutun rabin lokaci.

Dan wasan Ingila Luke Shaw da ke buga kwallo a Manchester United ya narka kwallon ta wuce ragar Gianluigi Donnarumma, minti biyu kacal da fara wasan wanda aka buga a filin Wembley da ke London.

Sai dai dan wasan Italiya Leonardo Bonucci ya farke kwallon a minti na 66, lamarin da ya sa wasan ya koma danye.

‘Yan wasan Roberto Mancini sun yi ta nuna alamun dari-dari a farkon wasan, amma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sun yi ta kai hare-hare.

Wannan shi ne karo na hudu da Italiya take lashe kofin gasar, wacce Ingila ba ta taba dauka ba.

Kiyasin da hukumar kwallon kafa ta duniya ta fitar a ranar 27 ga watan Mayu ya nuna cewa Ingila ce ta hudu a iya taka leda a duniya yayin da Italiya take mataki na 7.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: