Labarai

Isa Ali Fantami Bai Cika Sharudan Zama Farfesa ba~ Inji Dr. auwal Mustapha Imam

Na Rantse da Allah Isa Ali Shima yasan bai cika sharuɗan Zama Farfesa ba.
Auwal mustapha Imam yayi wankin babban bargo da Nasiha mai cike da girgizarwa zuwa ga Isa Ali Pantami akan matsayin Farfesa da a bashi. Dr Awwal mustapha Imam yace inda shine isa Ali Pantami wallahi Bazai karba ba. Zai mayar musu da kayan su ne. Idan kuɗi ya basu to yana mai bashi shawara ya ajiye musu kayan su domin koyi da managartan bayi masu Tsoron Allah. Da wasu daga cikin Daktoci wanda shi isa Ali Pantami ya sansu wajen taka tsantsan.

Prof. Isah Ali Pantami

Dakta ya kara da cewa wannan maganar ba Hassada ba ce..kiyaye martaban ilimi ne. Shima a lokacin da yake karatu bai karasa kaiwa matakin dakta ba. Idan a ko irashi da matsayin dakta kunya yake ji baya iya amsawa domin yasan cewa bai Chan-chanci matsayin ba a wancan lokacin. Amma a yanzu idan ba’a kirashi da Dakta ba har wani haushi-haushi yake ji. Inji Dakta Auwwa mustapha Imam.

Dakta Auwal Imam

Ku baiyana mana ra’ayoyinku kan hakan ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: