INEC Ta Tsayar Da Ranar Bawa Ganduje Da `Yan Majalisun Jiha Takardun Shaidan Cin Zabe


0 329

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaban wayar da kan masu zabe na INEC reshen jihar Kano, Mallam Muhammad Garba Lawal ya ce za a bawa zababen gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna da ‘yan majalisun dokokin 40 takardan shaidan lashe zabe a ranar Laraba na mako mai zuwa.

Shugaban sashin wayar da kan masu zabe da watsa labarai na INEC, Garba Lawal ne ya bayyana hakan yayin zantawar da ya yi da manema labarai a ranar Juma’a 29 ga watan Maris.

Garba ya ce ana sa ran kwamishinan INEC na kasa mai kula da jihohin Kano, Jigawa da Katsina, Injiya Abubakar Nahuche ne zai gabatar da takardun shaidan lashe zaben ga zababun shugabannin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Ganduje da sauran zabaun ‘yan majalisun dokokin jihar Kano 40 za su karbi takardun shaidan lashe zabe a ranar Laraba

Jam’iyyar APC ta lashe kujeru majalisar dokokin jihar 27 cikin 40 yayin da jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta lashe kujeru 13.

Gwamnan jihar mai ci yanzu kuma zababen gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ci galaba a kan abokin fafatawarsa na jam’iyyar PDP Abba Kabiru Yusuf da ratar kuri’u 8,982.
Baturen zabe na jihar Farfesa Bello B Shehu ya sanar da cewa Ganduje ya lashe zaben ne bayan an gudanar da zaben rabar gardama a jihar.

A jawabinsa da ya yi na samun nasara, Dr. Abdulllahi Umar Ganduje ya yi alkawarin cigaba da ayyukan da ya fara kuma ya ce zai yiwa kowa adalci a jihar.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.