Labarai

INDA RANKA: Matar Da Ta Auri Maza 3 Ta Ajiye Su Duk A Gida Daya Kuma Suna Jin Dadin Zaman Aure Da Ita

INDA RANKA: Matar Da Ta Auri Maza 3 Ta Ajiye Su Duk A Gida Daya Kuma Suna Jin Dadin Zaman Aure Da Ita

 

Wata mata mai suna Nellie, wacce ta shahara da kasancewarta hamshakiyar attajira mai sana’ar sayar da motoci, ta bazu a shafukan labarai, bayan da rahotanni suka ce ta auri maza uku da suke zaune a gida Daya a halin yanzu kuma suna farin cikin da aurenta.

 

Nellie, mahaifiyar yaya biyu, ta bar mutane da mamaki bayan ta ba da labarin yadda ta yi aure cikin farin ciki da mazanta uku Jimmy, Danny da Hassan.

 

Ta auri sirikinta ne bayan mutuwar mijinta da shekara takwas ya rasu a hatsarin mota kuma daga baya ta auri sauran mazan biyu.

 

Nellie dillaliyar motoci ce kuma tana ba wa dukan mazajenta uku da ba su da aikin yi kudade.

 

Wani abin kuma shine ta siyowa duka mazajen nata guda uku motoci, duk suna zaune a gida daya kuma duk suna kasancewa da ita.

 

Nellie tana da tabbacin cewa mazajenta ba za su iya yaudarar ta ba tunda suna farin ciki kuma suna iƙirarin cewa tana bi da su daidai.

 

Sun yi shekara uku suna zama tare kuma mazan sun ce hakan ya sa suka zama aminan juna. Girmama junan su shine ya sanya su zauna lafiya.

 

Daga Baba Waziri Net ✍️