Siyasa

inasaran Allah Zai Taimakeni in cika mafarkin yan Najeriya—Bola Tinubu

Zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Tinubu yace Allah Zai Taimakeni in cika mafarkin yan Najeriya.

 

Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, a yau Juma’a, ya bayyana cewa Allah zai taimake shi ya cika burin ‘yan Najeriya da burinsa a lokacin gwamnatin sa.

.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya kai shi ziyarar sanin ya kamata a fadar shugaban kasa, a Abuja gabanin kaddamar da shi.

 

Ya kara da cewa Allah zai sa shi cikin koshin lafiya ya kuma taimake shi ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa ya samu damar cika burin ‘yan Najeriya.

 

Ya ce, “Ka taimake ni Allah, in ɗauki nauyi, ka fuskanci ƙalubale, ka sa ni cikin koshin lafiya, don in iya cika buri da muradin miliyoyin jama’ar Nijeriya.