Inada Masu Leken Asiri a Fadar Shugaban Kasa – Nnamdi Kanu
An jiyo shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu a wata hira da aka yi dashi yana ikirarin cewa yana da ‘yan leken asiri a fadar shugaban kasa dake gayamai duk wani abu da gwamnati ke shirin yi.
Kanu dake gudun hijira a kasar Isra’ila ya bayyana cewa, ta hakane yake sanin abinda gwamnati zata yi ya kuma gayawa mutane.