-Advertisement-


Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Ina Tsoron Mutuwar Zakzaky A Hannun Gwamnati – Campbell


0 509

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ina tsoron mutuwar Zakzaky a hannun gwamnati – Campbell

Tsohon Jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, ya ce idan har Najeriya ta ci gaba da tsare shugaban kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi ta Shi’a (IMN) to za a iya samun rikici irin na Boko Haram.

Mr Campbell, wanda mamba ne a majalisar huldar jakandancin Amurka, ya ce idan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya mutu a hannun gwamnati to “komai zai iya faruwa a kasar”.

Sama da shekara biyu kenan gwamnatin Muhammadu Buhari na tsare da Sheikh Zakzaky da matarsa a wani kebabban wuri da ba a bayyana ba, duk da cewa kotuna da dama sun bayar da belinsa.

A watan da ya wuce ne gwamnatin jihar Kaduna ta tuhumi malamin tare da wasu mutum uku da laifuka takwas ciki har da kisan wani soja a shekarra 2015, lamarin da suka sha musantawa.

Sojan mai mukamin kofaral na cikin ayarin da ke tare da Hafsan Sojin kasa Janarar Tukur Burutai lokacin da suka yi arrangama da ‘yan shia a garin Zaria a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2015.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 324

- Advertisement -

Daga bisani kuma sojoji sun kai wa jagoran ‘yan Shi’a hari a gidansa da ke Zaria inda suka kashe mutum sama da 300.

Sai dai magoya bayan malamin sun ce mutanen da aka kashe musu sun doshi 1,000, sannan aka yi awon gaba da wasu da dama.

Tsohon Jakada Campbell ya ce ‘yan Shi’a a Najeriya “sun yi kama da Boko Haram ta fuskar kafa gwamnati”.

“Mun ga yadda gwamnatin kasar Iran ta nuna rashin jin dadinta lokacin da aka kama Zakzaky.
Ba mu sani ba ko kasar na tallafawa ‘yan Shi’ar Najeriya da kudade” in ji shi.

Mun san yana tsare ne a hannun gwamnatin tarayya.

Ya kara da cewa “gwamnatin na cewa ba za ta sake shi ba har sai gwamnatin jihar da ya sabawa ta yanke shawara, wato kenan gwamnatin jiha ce take tuhumar El-Zakzaky ba ta tarayya ba”.

Me zai faru idan ya mutu a hannun gwamnati? Inji Campbell

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.