SHIN WANE FARIN CIKI KUKE JI KO BAKIN CIKI RUBUTA RA AYINKA A KASA
Fitacciyar ‘yar wasan Kannywood, Hadiza Gabon da wasu masu shiryawa da ba da umarni a fina-finan Hausa za su je Amurka.
‘Yan Kannywood din za su halarci wani taron karawa-juna-sani na mako biyu ne, a wata makarantar koyar da dabarun shirin fim da ke katafaren cibiyar shirin fim ta LA Studios Center.
A ranar Talata 9 ga watan Fabarairu ne jaruman za su tashi zuwa Amurkan.
Sauran jaruman da za a yi tafiyar da su, su ne: Ali Nuhu da Hauwa Maina.
A cikin masu shiryawa da bayar da umarni kuwa, da akwai Hafizu Bello da Kamal Sani Alkali, da Nazifi Asnanic da Bello Mohammed Bello, da kuma Hassan Giggs.
A yayin ziyarar, za su ga yadda ake shirya fim na zamani, za kuma su koyi sababbin dabaru na shirin fim wanda zai taimaka wa fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood.
A hirar da BBC ta yi da Mohammed Sani, na kamfanin da ya shirya tafiyar ya ce, ziyarar hadin gwiwa ce da wani kamfani mai son taimakawa shirin fina-finai a Najeriya, musammnan wadanda ake yi da Hausa, saboda tasirinsu da kuma karbuwarsu a duniya.
Wannan ziyara ta zo ne a lokacin da ake shirin bikin bayar da kyatuttuka na Kannywood Awards a watan Maris, da kuma bikin cika shekaru 25 da soma fina-finan Hausa a Najeriya.
Add Comment