Kannywood

Ina Makomar Dalibai 101 Da Jarumi Adam A. Zango Ya Yi Ikrarin Daukar Nauyin Karatunsu?

Daga Indabawa Aliyu Imam

Kawo yanzu, shekara guda kenan da wani abu daga sanda fitaccen Jarumin finafinan Hausa Adam A. Zango ya shelanta daukar nauyin dalibai marasa galihu mutum dari da daya wanda yace ya kashe musu jumlar kudi miliyan har arba’in da bakwai.

Sai dai an sami manazarta da ‘yan jarida wadanda suka karyata ikrarin jarumin cewa batun daukar nauyin dalibai dari da daya ba gaskiya ba ne bisa wasu dalilai inda har suka kalubanci jarumin da ya nuna shaida ko hujjar biyan kudin da yayi ikrari, hujjar da jarumin ya kasa bayyanawa.

Sai dai shugaban makarantar ya tabbatar da sahihancin ikrarin Jarumi A Zango wanda makusantansa suka ce aminin jarumin ne kuma su biyun sun shirya wannan gidogar ne don cimma wasu burika.

Duk da ziyartar Masarautar Zazzau da jarumin yayi don bayyanawa marigayi sarkin Zazzau wannan alkhairi kawo yanzu bincike ya kasa samun daliban da aka ce an dauki nauyin karatun nasu ba su kadai ba har iyayensu, makusantansu da ma wadanda suka san su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: