Mahaifi ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Alhaji Musa Sale Kwankwaso ya ce duk wata irin karramawa ta duniya, hakika Ganduje ya yi masa a rayuwa.
Dan haka ne ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su sake zaben Dakta Abdullahi Umar Ganduje (Kadimul Islam) a matsayin gwamnan jihar Kano a zaben 2019.