-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Ina Farin Ciki Mun DaiDaita Da Shagari – Buhari


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana godiya ga Allah cewa dangantakar da ke tsakaninsa da marigayi Alhaji Shehu Aliyu Shagari tsohon shugaban kasar mai cikakken iko na farko ta gyaru.

Ya ce duk da bambancin ra’ayi a kan wasu batutuwa, amma sun yi nasarar gyara alakar da ke tsakaninsu.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar don bayyana alhininsa game da rasuwar Shehu Shagari.

Ya bayyana Shagari a matsayin kamilin mutum dan kishin kasa da ya bayar da gagarumar gudunmawa a fannoni da dama wajen ciyar da kasa gaba.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

- Advertisement -

Muhammadu Buhari ne dai ya jagoranci kifar da gwamnatin marigayi Shehu Shagari lokacin yana babban hafsan soja a 1983.

Sai dai a cikin sanarwar, Buhari ya ce mutuwar Shehu Shagari, wani babban rashi ne ga Najeriya.

A cewarsa, Najeriya ta yi asarar wata gada wadda ke hada dangantaka tsakanin tsoffin ‘yan kishin kasa da suka yi fafutukar kwato ‘yancin kai da kuma ‘yan baya.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: