A wani sabon sako da ya aikowa ‘yan Nijeriya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi cewa yana bukatar karin lokaci domin ya huta sosai, kamar yadda likitoci suka umarce sa da ya yi.
Shugaban ya aiko da sakon ne ta bakin masu taimaka masa akan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu da Femi Adesina.
Toh sai dai har yanzu fadar shugaban kasar ta gaza bayyanawa ‘yan Nijeriya abunda suka fi son sani, wato ainihin rashin lafiyar da ke damun shugaban kasar.
Da aka Tambayi Femi Adesina game da wannan, ya bayyana cewa ko likitoci ma doka ba ta basu damar bayyana abunda ke damun mara lafiyar da ke karkashin kulawar su ba.
Shugaban Buhari dai ya bar Nijeriya a ranar 19 ga watan Janairu domin ya yi hutu a birnin London da ke kasar Birtaniya, sannan ya yi amfani da damar wajen duba lafiyar sa.
Shugaban ya dage hutun sa da fari ne domin ya jira sakamakon wasu gwaje gwajen da yace likitoci sun yi masa, inda a yanzu kuma ya ce sakamakon gwaje gwajen na bukatar ya kara hutawa sosai.
Kafin ya bar Nijeriya dai shugaba Buhari ya mika mulki ga mataimakinsa, farfesa Yemi Osinbajo.
‘yan Nijeriya da dama na ci gaba da yi wa shugaban addu’o’in samun lafiya.
Add Comment