In da Kwankwaso ne ya je bikin rantsar da Tinubu dole su bar shi ya shiga rumfar manyan mutane mai gilashi ba ta gama-garin mutane ba saboda kwarjininsa – Inji Danzago
Ƙusa a jam’iyyar APC a Kano, Ahmadu Haruna Zago, ya bayyana cewa halin tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya janyo a ka wulakanta shi a wajen rantsar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa an hana Ganduje, da gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo shiga sashen manyan baƙi na musamman, wanda aka fi sani da VIP yayin bikin rantsar da shugaba Bola Tinubu a Litinin.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa an zaunar da manyan baƙi ne na musamman a wani ɓangare na gilashi yayin da wasu manyan mutane ke zaune a wasu rumfunan dandalin Eagle Square.
Rahoton BBC Hausa ya ce, Ganduje wanda ya isa rumfar manyan baƙi dauke da katin gayyata mai launin kore tare da matarsa, Hafsat Ganduje, sai jami’an tsaro su ka hana shi shiga.
Jami’an tsaron sun shaida wa Gwamna Ganduje cewa baki masu katin gayyata mai kalar gwal ne kadai za a baiwa damar shiga cikin rumfar VIP.
Sai dai kuma da ya ke tsokaci a kan lamarin, a wata hira da ya yi da Freedom Radio a Kano a jiya Talata da daddare, Zago, wanda aka fi sani da Danzago ya ce inda Rabi’u Musa Kwankwaso ne ba za a wulakanta shi haka ba.
A cewar sa, ko da babu kwarjini da cewa yayi suna a Nijeriya, idan da Kwankwaso ne ya je wajen sai an bar shi ya shiga saboda shi mutum ne da ya saiwa kansa daraja.
“Ina tabbatar maka babu wani immunity ko popularity, inda Kwankwaso ne ya je wallahi sai an bar shi ya shiga. Ba gidan glass ba ko gidan wuta ne sai an bar shi ya shiga.
“Mutum ne da ya saiwa kansa daraja. Ba ya sunƙume-sunƙume, ba ya yanke-yanke ba ya komai, shi yasa ya samu daraja, in ji Danzago.
Add Comment