Kiwon lafiya

Illoli 7 da amfani da kwanukar Roba wajen ci, ajiye abinci ko ruwan sha ke yi wa lafiyar dan Adam

Duk da cewa mafi yawa daga cikin mutane a gida, ofisoshi ko a wuraren siyar da abinci suna amfani da kwanuka, kofuna da cokular roba, da yawa daga cikinsu ko kuma dukkansu basu da wani masaniya akan illolin da ke tattare da yin amfani da kwanukan roba.

Wani dan majalisa mai wakiltar jihar Edo, mai suna Serigius Ogun ya kawo wata kudiri na neman a rage yawan amfani da roba wajen ajiye abinci ko ruwar da muke sha.

A bayanansa a zauren majalisar Serigius Ogun ya ce zuba abinci musamman idan ya na da zafi a cikin roba ko kuma shan ababen sha kamar ruwa ko kuma lemun zaki wanda ya dade a rana na iya raunana jikin dan Adam.

Bayan tattaunawa da muhawara da ‘yan majalisun su kayi sun amince da gaiyatar ministan kiwon lafiya saac Adewole da ya bayyana agaban majalisar domin wayar musu da kai akan wannan kudiri.

Masana sun bada bayanai akan illolin yawaita amfani da kwanuka, kofuna da gorar roba kamar haka;

 

1 – Dukkan Roba na dauke da wani kemikal mai suna ‘Toxic Compound’ wanda amfani dashi yakan yi sanadiyyar sa a kamu da cututtuka kamarsu cutar daji , cutar tabuwar hankali, cutar ciwon kafa wanda ake kira da Arthritis, cutar bugawan zuciya da cutar rashin karfin idanu.

2. Mafi yawa daga cikin manyan masana’antu na cewa akwai robar da ba ya illata jikin mutum musamman robobin da suke da sinadarin Bisphenol A (BPA) amma sun ce robar da ke da sinadarin Bisphenol S (BPS) ne ke kawo lahani a jikin mutum.

Bincike ya nuna cewa duk robar da aka yi shi da Bisphenol A ko Bisphenol S (BPS) na yin lahani ga jikin mutum.

3. Yawan amfani da roba wajen cin abinci ko adana ruwan sha ko lemu da ake sha na kawo matsalar rashin haihuwa; Bincike ya nuna cewa sinadarin nan dai wanda ake kira da Bisphenol A (BPA) da ke cikin roba na iya hana mata haihuwa idan ana yawan amfani da shi. Ko kuma a haihu nakasasshen yaro.

4. Yawan amfani da roba wajen cin abinci ko adana ruwa sha da muke sha na kawo kiba a jiki.

5. Shi kanshi robobin da ake amfani dasu kuma a zubar dasu na lalata muhallin mu da kasar da muke takawa. Idan haka ya ci gaba kasar ma zai gagara zama. (http://www.foodmatters.com)

Daga karshe dai masana sun ba da shawara da mai makon Amfani da kwanuka, gora ko kofunan roba a nemi wadanda ba a yi su da roba ba domin gujewa fadawa irin wadannan matsaloli.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.