-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Idan N-Power Ya Koma Siyasa Za Mu Sa A Soke Shi – Shehu Sani


1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Majalisar dattawa a Najeriya ta ce tana gudanar da bincike game da zargin ‘yan siyasa suna amfani da shirin N-Power na tallafawa al’umma da kudade domin zaben 2019.
Majalisar ta kafa wani kwamiti domin binciken zargin cewa shirin da ke bayar da tallafin kudi ga talakawa yanzu ya koma wata hanyar da ‘yan siyasa suke raba wa magoya bayansu a yayin da zabe ke karatowa.
Sanata Shehu Sani wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PRP ya shaida wa BBC cewa idan har suka gano shirin na N-Power ya koma na siyasa za su bukaci a dakatar da shi.

Za mu bukaci a tsaida raba wadannan kudi idan har muka gano ‘yan siyasa ke raba wa magoya bayansu,” in ji shi.
Sai dai kuma gwamnatin tarayya ta yi watsi da zargin, inda Barista Ismail Ahmad, babban mai bai wa shugaba Buhari shawara kan shirin tallafa wa al’umma, ya ce wannan kawai wani yunkuri ne na kushewa da cin zarafin shirin.
Ya ce shirin ba ruwan shi da wata jam’iyya, domin kasuwa a ke shiga a zakulo masu kananan sana’oi domin ba su tallafi ba tare nuna bambanci ba.
Ya kuma ce a shirye suke su je su kare kansu idan har kwamitin bincike da majalisar dattawa ta kafa ya gayyace su domin gurfana a gabansa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 660

- Advertisement -

Sanata Shehu Sani ya ce sun samu korafe-korafe daga jama’a da dama cewar ana karkatar da kudaden ana rabawa magoya bayan gwamna a jiohihi da ‘yan majalisu da wasu ‘yan siyasa maimakon raba wa talakawa da aka bullo da shirin domin su.
Ya ce ba an kafa wannan tallafi ba ne don taimakawa ‘yan siyasa, an kafa shi ne domin taimakon talakawa da ‘yan kasuwa.
Ya kuma ce rahotannin da suka samu sun bayyana yadda fom da ake raba wa ke fitowa daga jam’iyar siyasa da jami’an gwamnati.
Kuma a kan haka ya ce idan har suka tabbatar da gaskiyar zarge-zargen, to za su bukaci a tsaida raba kudaden tallafin.
“Idan za a yi shi kan gaskiya ne to sai dai a ba kowa, mace ko namji ko tsoho ko matashi da ke bukatar taimako”
“Idan ba haka ba ya kasance ba ya da bambanci da abubuwan da suka faru a gwamnatin da ta shude inda wasu suka yi amfani da damar domin azurta kansu da abokansu da ‘yan uwansu.” in ji shi.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: